Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan.
An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin Darfur.
A farkon wannan watan ne kotun ta ICC ta samu kara da ke da alaka da ta’addancin da aka yi a yankin Darfur a lokacin rikicin 2003-2004. An samu Kushayb da laifin bayar da umarnin kisa ga jama’a tare da kashe fursunoni biyu da gatari da kansa.
Lauya mai gabatar da kara Julian Nichols, yana magana a yayin zaman yanke hukunci na musamman, inda ya fallasa tare da kuma caccakar Kushayb a matsayin mai kisan kai da gatari. Ya ce Kushayb da kansa ya yi amfani da gatari ya kashe mutane biyu kuma ya kasance a sahun gaba wajen cin zarafin da aka yi a yankin Darfur fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Mai gabatar da kara ya jaddada girman laifuffukan, yana mai nuni da irin rawar da Kushayb ya taka a ta’asar da aka aikata a farkon shekarun 2000 a matsayin shaida cewa ya kamata a yanke masa hukunci mafi tsanani a kotun.