Masu Gwagwarmayan Musulunci Sun Kai Hare-Hare Kan Wurare A HKI

Gamayyar kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bada sanarwan kai hare-hare a kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye. Tashar

Gamayyar kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bada sanarwan kai hare-hare a kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar masu gwagwarmayan na fadar haka a jiya Lahadi, ta kuma kara da cewa ta yi amfani da makaman ‘Drones’ ko jiragen yaki masu kunan bakin wajen a wadannan hare-hare.

Hashdusha’abi wacce ta kasance laimar kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar ta Iraqi sun bayyana cewa sun kai hare-haren ne saboda tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI yan mamaye suke kashewa tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 a zirin gaza.

Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudawa sun kashe falasdinawa kimani 44,000, mafi yawansu mata da yara. Banda haka akwai wasu kimani 104 wananda suka ji Rauni. Har’ila yau akwai marayu da mata zawarawa da suka bari.

Hashdushaabi ta kammala da cewa zata ci gaba da wadannan hare-hare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments