Amurkawa masu goyon bayan Falasdinu sun gudanar da gangami a unguwar manhatan na birnin Nuyork don neman sakin Mahmoud Khalil daya daga cikin masu gwagwarmaya kan tafarkin samun yencin Falasdinawa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kama Mahmoud Khalila da kuma tsareshi ya ingiza matasa da dama a Amurka suka nuna goyon bayansu a gareshi, wasu kuma suka fito zanga-zangar neman a sake shi.
Mahmoud Khalil dai, ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Colombia na birnin News na kasar Amurka. Sannan ya shahara da goyon baya ga al-ummar Falasdinu. Banda haka yana da ‘Green Card wanda ya bashi damar zama a kasar Amurka na dindin din. Amma a rahotannin da suke fitowa gwamnatin kasar tan son soke dakardun nasa don basu damar korarsa daga kasar Amurka.
Gwamnatin shugaba Trump ta yanke Dalar Amurka miliyon $400 kasan Jami’ar Colombia saboda tursasa mata ta yi fada da wadanda ya kira, masu nuna kin yahudawa