Wani mataki kwatsam a Faransa ana neman tsige shugaban kasar Emmanuel Macron daga mukaminsa
Jam’iyyar France Insoumise daga jam’iyyar Popular Front mai ra’ayin rikau ta sanar da cewa za ta fara wani yunkuri karkashin sashi na 68 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya tanadi yiwuwar tsige shugaban kasar Emmanuel Macron daga kan mukaminsa bayan cire jam’iyyar daga kafa gwamnati.
Manuel Bompard mai shiga tsakani a jam’iyyar “France Insoumise” a sanarwar da ya fitar a shafin dandalin “X” ya bayyana cewa: Macron ya ki amincewa da nada Lucie Castet a matsayin fira minista, don haka wakilan jam’iyyar “France Insoumise” za su gabatar da daftarin kudurin neman tsige Macron ga Majalisar Dokoki ta kasar Faransa a karkashin sashi na 68 na Kundin Tsarin Mulkin kasar, kuma duk wata shawara ta dan takarar fira minista idan ba Lucie Castet ba, zai fuskanci rashin kada kuri’ar amincewa da Macron.