Masharhanta sun bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta fuskanci mummunan dukan girma daga Hizbullahi

Tun bayan da ‘yan gwagwarmayaMusuluncin suka shiga yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila domin taimakawa ‘yan uwansu a Gaza a watan Oktoban shekara ta 2024,

Tun bayan da ‘yan gwagwarmayaMusuluncin suka shiga yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila domin taimakawa ‘yan uwansu a Gaza a watan Oktoban shekara ta 2024, ‘yan gwagwarmaya suka din ga janyo dimbin hasara ga gwamnatin ‘yan sahayoniyya, inda hare-haren ‘yan gwagwarmaya suka janyo hasarori da barna masu raɗaɗi a matakin sansanonin soji da helkwata masu mahimmanci na yahudawan sahayoniyya.

Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kai hare-hare kan manyan sansanonin soji a arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila ire-iren sansanin sojin saman “Ramat David Air Base, wanda ya yi sanadin lalata jiragen yaki tare da lalata kayayyakin soji.

An harba makamai masu linzami kan sansanin Zikhron Ya’akov wanda ya kai ga lalata wasu motocin soji.

Kai jerin hare-hare kan sansanin Tel Hashomer, sansanin horarwa da cibiyar ayyuka, wanda ya dakile ayyukan soji a yankin.

Hare-hare da makamai masu linzami kan hedkwatar cibiyar leken asiri ta Mossad a tsakiyar birnin Tel Aviv tare da mummunar barna a wurin, kai hare-haren makamai masu linzami kan hedkwatar rundunar sojan Golani wadanda suka yi sanadin halaka da jikkatar sojoji tare da lalata motocin soji.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments