Masar ta yi watsi da wasan sada zumunta da Zambia kan  Isra’ilawa na horar da ‘yan wasan kasar

Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada

Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba.

Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta.

Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin  Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga karshen watan Disamba zuwa tsakiyar watan Janairu.

Zambiya sau da yawa tana fafatawa da kasashen Larabawa da na musulmi ba tare da yin la’akari da alakar hakan da Isra’ila ba, sai dai kuma jami’an Masar sun bayyana cewa basu da matsala da mai horar da ‘yan wasan Zambia ko mataimakinsa wadanda Isra’ilawa ne, amma sun ba da misali da yakin da ake yi a Gaza da kuma manyan laifukan da Isra’ila take tafkawa kan fararen hula da cewa abu ne mai sosa rai, wanda kuma wadannan abubuwa su ne manyan dalilai na soke gasar.

Ana ci gaba da bincike kan “Isra’ila” a fagen kwallon kafa, a baya-bayan nan lokacin da kungiyar masu horar da ‘yan wasa ta Italiya (AIAC) ta yi kira ga FIFA da UEFA da su dakatar da “Isra’ila” daga gasar kwallon kafa ta kasa da kasa, saboda yakin da ake yi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted