Masar Da Kuwaiti Sun Yi Allawadai Da Kiraye-kirayen ” Isra’ilawa” Na Rusa Masallacin Kudus

Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin

Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi.

Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar ne bayan da wasu yahudawa su ka watsa wani faifen bidiyo na tarwatsa masallacin Kudus da kuma maye gurbinsa da gina wajen bautar yahudawa.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana cewa: “Jamhuriyar Larabawa ta Masar tana yin tir da kakkausar murya akan kiraye-kirayen da masu tsattsauran ra’ayin ‘yan share wuri zauna suke yi na tarwatsa masallacin Kudus.

Haka nan kuma Masar din ta yi kira da a kawo karshen keta hurumin masallacin Kudus wanda yake tsokana ce ga al’ummar musulmi.

Ita ma kasar Kuwaiti ta fitar da bayani da a cikin ta yi tir da kora zuwa ga rusa masallacin Kudus da kungiyoyin ‘yan share wuri zauna suke yi. Ta kuma kara da cewa, kiraye-kiraye irin wadannan tsokana ce ga al’ummar musulmin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments