Masar: An Kawo Karshen Taron Kasashen Larabawa Na Musamman Akan Gaza

Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda

Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza.

Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila.

Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban.

Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da  shirin na sake gina Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments