Manya Manyan Jami’an gwamnatoci Da Kungiyoyi Kimani 65 Suka Zo Tehran Don Yin Bankwana Da Shahid Ra’isi

Bayan sallar Jana’iza wanda jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee ya yiwa shugaban kasa shahida Ibrahim Ra’isi, da

Bayan sallar Jana’iza wanda jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee ya yiwa shugaban kasa shahida Ibrahim Ra’isi, da ministan harkokin wajensa Dr Hussain Amir Abdullahin, tare da sauran shahidan  hatsarin jirgin sama na ranar Lahadi, a masallacin jumma’a dake cikin Jami’an Tehran, moliyoyin mutanen kasar Iran a nan birnin Tehran sun yiwa gawakin shahidan rakiya zuwa dandalin Azadi da ke tsakiyar Tehran.

Banda haka manya manyan kabi daga kasashen duniya kimani 65, wadanda suka hada da shuwagabannin kasa, Sarakunan, shuwagabannin gwamnati, sun yiwa shahidan addu’a samun raham,ar Allah, da kuma girmamasu.

Shugaban kasar Tunisia Dr Kais Sa’ida na daga cikin shuwagabannin kasashen da suka yiwa shahidan addu’a, sai Sarkin Qatar Taminin bin Alithani sarkin, firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia Assudani, mataimkin shugaban kasar Chaina, shugaban majalisar Duma na kasar Rasha da kuma wakilan sauran kasashen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments