Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta dakatar da gidan talbijin na Faransa LCI daga aiki a kasar tsawon watanni biyu, inda ta zarge shi da yin “zarge-zarge na karya ” game da rundunar sojin kasar da abokansu na Rasha.
“An dakatar da gidan talbijin na LCI television daga watsa labarai na rediyo da talbijin a Mali tsawon watanni biyu” daga ranar 23 ga watan Agusta, a cewar hukumar da ke sanya ido kan kafafen watsa labarai ta Mali a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.
A cewar hukumar da ke sanya ido kan kafofin watsa labarai, wani mai sharhi a gidan talbijin na LCI ya yi zarge-zarge masu cike da karya a wani shiri da ake kira “Wagner Decimated in Mali: the Hand of Kyiv”.
Hukumar ta ce shirin na kunshe da “kalamai na cin zarafi da karairayi game da rundunar sojojin Mali da abokan hadin-gwiwarta na Rasha”.
Dama tun kafin hakan sojojin dake mulki a Mali, sun dakatar da fitattun kafofin watsa labaran Faransa irin su RFI da France 24 a watan Afrilun 2022, da kuma France 2 a farkon shekarar 2024.