Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a tsangayar fina-finai ta Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu na kasar Rasha, Olga Lyubimova, mataimakin shugaban kasar Rasha, Vladmir Medinsky sai kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Rasha Kazem Jalali.
Shugaban Tsangayar FIna-finai ta Eurasia, Nikita Mikhalov ya jinjina wa Majid Majidi saboda fina-finan da ya yi da hakan ya sa aka ba shi kyauta ta musamma da ita ce lambar yabo ta “ Dimond Butterfly”.
A jawabin da ya gabatar, Majid Majidi ya bayyana cewa; Mafi yawancin fina-finan da yake yi, suna da alaka ne da kananan yara da kuma matasa. Haka nan kuma ya ambaci da yin ishara da kananan yaran Gaza wadanda ake zalunta, yana mai fatan ganin zaman lafiya mai dorewa ya mamaye duniya.
Gabanin mika masa lambar yabon, an nuna wasu daga fina-finan da Majidi ya shirya da su ka hada da fim din tarihin manzon Allah ( s.a.w) mai taken; Muhammad; Manzon Allah.
Kimar lambar yabon da aka bai wa Majid Majidi dai ta kai dalar Amurka miliyan daya, da wani dan kasar China mai shirya fina-finai Xh Zheng ya samu,saboda fim dinsa mai taken: “Against the Current”.
Shi dai Majid Majidi an haife shi ne a Tehran a 1959, yana kuma daya daga cikin fitattun masu shirye-finai a Iran.
A shekarar 1997 fim dinsa mai taken; The children of Heaven,’ ya shiga takarar samun kyautar fina-finai ta Amurka.
Wasu fina-finansa da su ka yi suna a duniya sun hada; The Color of Paradise (1999), sai Baran (2001).
Fina-finansa dai sun fi mayar da hankali ne akan matsaloli na kananan yara, talaucii, jajurcewa a gwagwarmaya da hakan ya sa shi yin fice a cikin gida da kuma a duniya.