Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, majalisar dokokin kasar za ta duba wani batu na ayyana sojojin kasashen turai a matsayin kungiyoyin ta’addanci.
Wannan na a matsayin martanin Iran ne biyo bayan matakin da kasashen turan suka dauka na ayyana dakarun kare juyin juya halin Musulinci na kasar ta Iran a matsayin ‘yan ta’adda.
Araghchi ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da tashar talabijin ta CNN sashen Turk yayin da yake ziyara a Turkiyya.
Da yake amsa tambaya game da matakin na EU na ayyana IRGC a matsayin ‘yan ta’adda kwanan nan, Araghchi ya ce “Tarayyar Turai ta yi babban kuskure na dabaru ta hanyar ayyana (IRGC) a matsayin kungiyar ta’addanci.
“IRGC ta taka muhimmiyar rawa a yaki da kungiyar IS da ‘yan ta’adda a yankin.
Dole ne in ce da ba don IRGC ba, da Turawa za su fuskanci ISIS a yau a Paris ko wasu biranen Turai.
A halin da ake ciki yayin da wasu kasashen yankin ke kokarin hana jefa yankin cikin wani sabon rikici, kasashen Turan a nasu bangaren suka kara ruruta wutar,” in ji babban jami’in diflomasiyyar Iran.