Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da kasashe biyu da zai kai ga kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, da sake gina Gaza, da tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.
Sanarwar karshe da taron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan sasanta rikicin Falasdinu cikin lumana ya sanar da amincewar kasashen duniya kan daukar matakai na bai daya don kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Gaza da kuma bin hanyar warware matsalar samar da kasashe biyu a matsayin zabi daya tilo na samun daidaito a yankin.
A cikin wani abin da aka fi sani da “Sanarwar New York”, shugabanni da wakilan da suka taru a Majalisar Dinkin Duniya sun amince da yin aiki don samar da adalci dawwamamme, da kuma daidaita rikicin Falasdinu da Isra’ila, suna mai jaddada cewa al’amuran baya-bayan nan sun nuna mummunan hasarar bil’adama da kuma mummunan sakamakon rikicin da ake ci gaba da yi.