Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: ‘Yan Sudan Miliyan 30 Ne Suke Bukatar Agajin Jin Kai

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara

Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula, mutane da dama suna gudun hijira da kuma samun karuwar matsalolin bukatun jin kai.   

Tondlana ya nuni da cewa: Akwai matsalolin tsaro a Sudan saboda hau-hau-hawar farashin kayayyakin bukatu saboda rashin zaman lafiya a kasar.

Dangane da yanayin yunwa da aka shelanta a wasu yankunan, ya yi gargadin cewa lamarin na kara ta’azzara saboda fadan da ake fama da shi a yankunan da suka hada da yankunan Darfur da Kordofan da Al-jazira, ya kuma kara da cewa: Ba su samun damar isa ga mutanen da ya kamata su kai musu agajin jin kai da neman inganta rayuwarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments