Majalisar Dinkin Duniya ta karyata zargin ‘yan sahayoniyya cewa: Akwai sansanonin soji a cikin filin jirgin saman birnin Sana’a na kasar Yemen
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen, Julian Harness, ya musanta zargin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi na cewa: Filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yemen yana dauke da wasu barikokin soji, bayan da ya tsallake rijiya da baya a harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan filin jirgin saman.
Harness ya jaddada cewa: Filin jirgin saman, wani wuri ne na farar hula da Majalisar Dinkin Duniya ke amfani da shi da kuma wasu kungiyoyi irin su kungiyar kasa da kasa ta Red Cross, baya ga kasancewarsa waje na musamman na gudanar da jigilar fararen hula zuwa tafiye-tafiye, bisa la’akari da cewa: Bangarori biyu masu rikici da juna a kasar da kada su bari a kai hari kan filin jirgin.
Harness ya yi magana game da hare-haren da aka kai kan filin jirgin a lokacin da yake cikinsa tare da shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom da sauran ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya, yayin da aka yi luguden bama-bamai a cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama, ya kuma kara da cewa an mayar da tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya zuwa gudanar da zirga-ziurgansu a cikin motocin masu sulke saboda dalilai na tsaro.