Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaron Iraki Ya Gana Da Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Iran

Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin

Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran

Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya ci gaba da ziyararsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda ya gana da tattaunawa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran.

Qassem al-Araji mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya gana da Manjo Janar Seyyed Abdolrahim Mousavi, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi moriyar kasashen biyu.

A yayin ganawar, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci.

Manjo Janar Mousavi ya kara da cewa, da a ce hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai kan Iran bai faru ba, to tabbas burin Amurka na sarrafa sararin samaniyar Iraki bai fito fili ga kowa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted