Mai Ba Da Shawara Ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Matsayin Iran Na Taimakawa Siriya

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Iran zata ci gaba da taimakon Siriya ta kowane bangare Mai ba

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Iran zata ci gaba da taimakon Siriya ta kowane bangare

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran kan harkokin kasa da kasa Ali Akbar Velayati ya ce: Ba su yi tsammanin Turkiyya za ta fada cikin tarkon da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka dana mata ba.

Velayati ya ci gaba da cewa: Suna fatan Hakan Fadan Ministan harkokin wajen Turkiyya a matsayinsa na kwararre a fannin leken asiri da harkokin waje zai iya gyara wasu kura-kurai da manufofin harkokin wajen Turkiyya da aka yi. Amma Iran ba ta yi tsammanin cewa Turkiyya da ke da tarihin Musulunci za ta fada cikin tarkon da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka shirya mata ba.

Velayati ya kara da cewa: Abin mamaki ne yadda ake aikata irin wadannan muggan ayyuka da sunan al’ummar Turkiyya, wadanda a tsawon tarihi suka tsaya tsayin daka kan kare matsayinsu na Musulunci da imani.

Ya ci gaba da cewa: A wani lokaci, wani gungun yahudawan sahayoniyya sun je wajen Sultan Abdul Hamid Al-Othmani domin neman sayan Falastinu domin kafa kasar Yahudawa a cikinta, inda martaninsa wani bayani ne na tarihi da ke cewa: “Ba a taɓa yin wani binciken gawar mutum matukar yana raye ba”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments