Mahukuntan Masar Sun Ce An Kawo Karshen Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza Babu Cimma Matsaya

Gwamnatin Masar ta sanar da cewa: An kawo karshen zaman tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ba tare da cimma matsaya ba Majiyoyin tsaron Masar sun

Gwamnatin Masar ta sanar da cewa: An kawo karshen zaman tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ba tare da cimma matsaya ba

Majiyoyin tsaron Masar sun sanar a cikin daren jiya Lahadi wayewar safiyar yau Litinin cewa: An kawo karshen zaman tattaunawan da aka yi a birnin Alkahira dangane da tsagaita bude wuta a Gaza.

Kafofin yada labaran Amurka sun ambato wasu majiyoyin tsaron Masar guda biyu na cewa: Tattaunawar tsagaita wuta tsakanin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba.

Majiyoyin biyu na Masar sun yi nuni da cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da haramtacciyar kasar Isra’ila ba su amince da mafi yawa daga cikin hanyoyin da masu shiga tsakani suka gabatar ba.

Daraktan hukumar leken asiri ta CIA, William Burns, da fira ministan Qatar Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani, da daraktan hukumar leken asirin Masar, Abbas Kamel, duk sun halarci zaman taron na Alkahira a jiya Lahadi.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments