Mahajjata aikin hajjin bana suna ci gaba da tururuwa zuwa tsayiwar Arafat a yau Alhamis
Mahajjata na ci gaba da tururuwa zuwa Arafat domin gudanar da muhimmin rukunnan aikin Hajji.
Mahajjata suna gudanar da ranarsu tun daga ketowar alfijir har zuwa bayan sallar isha’i a filin Arafat, bayan sun gudanar da ibadar ranar Tarwiyah, wadda mahajjaci ya yi a Mina, yana taqaita salloli ba tare da hada su ba.
A safiyar rana ta goma, mahajjata za su sake komawa Mina don jifan Jamarat al-Aqaba, kafin su yi aski ko saisaye, su yanka dabbar layya, Sannan su nufi dakin Ka’aba domin yin Tawafin Hajji.