Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro wanda ya bude bikin baje kolin littatafai na kasa da kasa a kasarsa, ya yi jinjina ga Imam Khumaini  (

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro wanda ya bude bikin baje kolin littatafai na kasa da kasa a kasarsa, ya yi jinjina ga Imam Khumaini  ( r.a) da kuma jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa, A yayin bikin bude taron baje kolin, shugaban kasar na Venezuela ya bayyana girmamawar da yake yi wa jagoran juyin musulunci, tare da yin ishara da ganawarsu a shekarun 2000 da 2010.

Haka nan kuma shugaban kasar ta venezuella ya bayyana yadda ya ga al’adu da ci gaban al’ummar Iran da su ka ja hankalinsa da burge shi matuka.

Bugu da kari shugaba Maduro ya bayyana zurfin hikimar da ya gani a tare da jagoran juyin musulunci,  da kuma yadda yake kare tsarin jamhuriyar musulunci da ci gaba da wanzuwarsa a cikin nutsuwa, hakuri, juriya da kuma tsayin daka.

Har ila yau, shugaba Maduro ya yi ishara da yadda Iran take cika alkawalinta a fagen kawancenta da kasarsa Venezuela.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments