Kungiyar samarin kasar Madagascar mai suna “Z Generation” ta yi kira ga mutanen kasar da su fito kwansu da kwarkwatrsu domin yin zanga-zanga akan gwamnatin Andry Rajolen da kuma yin zaman dirshen a tsakiyar babban birnin kasar.
Sai dai kuma a wani yunkuri na shanye fushin al’ummar kasar, fadar shugaban kasa ta bude kafar sauraron ra’ayin mutane da kuma kokensu daga ciki har da batun rashin aikin yi ko kuma wasu ‘yan’uwansu da ake tsare da su.
Tattaunawar da aka yi a fadar shugaban kasar an nuna ta talabijin din kasar, da manazarta su ka bayyana shi da tattaunawa ta kasa.
Kungiyar samarin kasar ta Magadishu sun ki halartar taron na fadar shugaban kasa tare da bayyana shi da wasan kwaikwayo. Sai dai kuma wasu daliban da su ka je fadar shugaban kasar sun yi suka aka yadda cin hanci da rashawa ya mamaye cibiyoyin hukumar kasar.
Kusan a kowace rana ta Allah ana yin Zanga-zangar a cikin garuruwan kasar domin nuna kin jinin gwamnati. Ya zuwa yanzu an kashe mutane 22 da kuma jikkata wasu 100.
Ita dai kungiyar ta samarin kasar “Generation Za” ba ta yin kira ga shugaban kasar da ya sauka, suna son kawo gyara ne. Tana kuma samun cikakken goyon baya kungiyoyin 20 na kasar da suke son ganin ana girmama ‘yancin al’umma, sannan kuma shugaban kasar ya fito ya nemi gafafar mutanen kasar akan kura-kuren da ya tafka.