Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa.
Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar.
Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba.
Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran.
Asghar Jahangir ya bayyana cewa wadannin yan liken asiri daga kasar Burtania, suna aikin leken asirin su ne da sunan bincike a wata Jami’a a cikin kasar, amma duk lokavinda suka fito sais u aikawa cibiyoyinsu a kasashen yamma da sakonni.