Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa 52,495
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a jiya Asabar 3 ga watan Mayu, shekara ta 2025 cewa: Falasdinawa 77 ne da suka yi shahada da suka hada da gawarwakin mutane 7 da aka gano, da kuma wasu mutane 275 da suka jikkata an kai asibitoci a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a cikin rahotonta na kididdiga ta yau da kullum kan adadin shahidai da jikkata sakamakon hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza: Har yanzu akwai adadin wadanda abin ya rutsa da su a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farar hula sun kasa kai musu dauki.
An ba da rahoton cewa adadin wadanda suka yi shahada a harin ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila ya karu zuwa shahidai 52,495 da kuma jikkata 118,366 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta shekara 2023.
Ma’aikatar ta yi nuni da cewa adadin wadanda suka yi shahadada jikkata tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025 ya kai (Shahidai 2,396, da jikkatan 6,325).