Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fidda rahoton, wanda ya nuna cewa sojojin HKI sun shafe iyalai kimani 1,400 a gaza tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a cikin shekara daya da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto rahoton yana cewa, iyalai kimani 1,410 ne sojojin yahudawan suka shafe daga doron kasa, wato babu mutum guda da ya rage a cikin dangin.
Rahoton ya kara da cewa, yawan mutanen da suka yi shahada a cikin wadannan iyalai sun kai 5,444.
Banda haka iyalai 3,463 ne mutum guda-guda suke rage a cikinsu, a yayin da wasu 2,287 kuma suke da fiye da mutum daya daga cikinsu da suka rage a cikin iyalin.
Kamfanin dillancin labaran WAFA na Falasdinawa ya bayyana cewa sojojin HKI sun ci gaba da Ruwan Boma bomai a arewacin zirin gaza a jiya Talata. Labarin ya kara da cewa boma-bomai sun fada kan gidaje da dama a garin Jabalia a jiya Talata, inda mutane da dama suka ji Rauni.
Kungiya mai kula da fararen hula a Gaza ta bayyana cewa mutanen 7 ne aka tabbatar da shahadarsu a hare haren na jiya Talata.