Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Gayyaci Jakadun Kasashen Turai Don Gargadarsu

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai zuwa ma’aikatar Bayan katsalandan din da ke kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai zuwa ma’aikatar

Bayan katsalandan din da ke kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawan yankin Tekun Farisa (GCC) da kungiyar tarayyar Turai suka yi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci jakadu da shugabannin tawagogin kasashen kungiyar ta Tarayyar Turai tare da mika musu takardar nuna rashin amincewa mai kakkausar murya kan goyon bayan da’awar karya mara tushe. Sanarwar ta tabbatar da cewa Iran ba za ta tsaya tana cece-kuce ba kuma tana nan matsayinta kan mallakar tsibiran Iran guda uku.

Bayanin baya-bayan nan da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin Tekun Pasha da kungiyar tarayyar Turai suka fitar sun jaddada da’awar cewa tsibiran uku ba mallakin Iran ba ne, wanda ya hada da zarge-zarge marasa tushe dangane da tsibiran guda uku da kuma shirin makamashin nukiliyar Iran, lamarin da ya haifar da rashin gamsuwa ga ma’aikatar harkokin wajen Iran.

Majalisar hadin gwiwar kasashen Larabawan yankin Tekun Pasha (Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait, Oman, Qatar) da kungiyar Tarayyar Turai sun fitar da sanarwa a ranar Litinin a taronsu na 29, inda suka jaddada bukatar dakatar da shirin Iran na samar da makamai masu linzami da kuma hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments