Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna.

A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana ci gaba da fitar da karin “hotunan tauraron dan adam don yada tsoro da fargaba kan Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, inda ake murguda gaskiya zuwa karya.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a matsayinsa na mai neman kawo cikas da zagon kasa, ya yi amfani da dukkan tsoffi da sabbin ma’aikatan da ya dauka a matsayin wani bangare na manufofinsa na “kayyade ayyuka ga Trump.”

Araghchi ya ce: A wannan karon, Netanyahu ya koma yin amfani da bayin Saddam Hussain ‘yan kungiyar ta’addanci ta “MKO” da suka kasance kaskantattu su na shirya masa karairayi kan Shirin nukiliyar Iran, inda dogaro da rahotonnin kungiyar “MKO” babbar alama ce ta yanke ƙauna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments