Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da batun warware takaddamar shirinta na makamshin nukiliay.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ya zo ne a matsayin mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka da ta ce: A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 2025 ne shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasa, inda ya ba da umarnin sake farfado da manufar mafi girman matsin lamba kan al’ummar Iran. Gwamnatin Amurka ta yi ikirarin sake farfado da manufar matsin lamba, duk da cewa siyasarta ta baya ta takunkumin kan Iran bata daina aiki ba kuma a halin yanzu ta jaddada aniyarta ta kara tsananta matakan takunkumin kan Iran a wannan lokaci.