Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar.
Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a. Ya kuma kara da cewa, lalle tawagar kasar Iran a tattaunawar suna ci gaba da tattaunawa, sannan suna matukar iyawarsu don kare hakkin Iran na mallakar Fasahar Nukliya wacce take da matukar muhimmanci.
Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran jami’an gwamnati suna sanya ido suna kuma kula da yadda tattaunawar take. Sannan ko way a san cewa wannan tattaunawar tana dimfare da makaman JMI ganin yadda kasar Amurka take barazanar faraway Iran da yaki sannan tana karawa kasar Takunkuman tattalin arziki ana cikin tattaunawar.
Har’ila yau limamin yana yi magana dangane da ranar ‘Malami” a kasar Iran wanda yayi dai-dai da ranar shahadin daya daga cikin jaga-jigan malaman da suka jagoranci juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979. Wato Aya. Shahid Murtada Muttahari.
Wata batacciyar kungiyar wacce ake kira furkan ce ta kashe Aya. Shahid Muttahari wataki bai 80 da nasarrar juyin juya halin musulunci a kasar.