Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza, kuma a gaggauwa kawo karshen kissan falasdinawa da kuma bude kofofin shigar da agaji zuwa cikin yankin. Inda miliyoyin Falasdinawa daga ciki har da yara miliyon guda suke mutuwar yunwa ga kuma kissa da makami ta sama.