Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa, wani babban kwamandan kungiyar ya yi shahada a wani hari da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai ta sama a kudancin Lebanon.
A cikin sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, kungiyar Hizbullah ta tabbatar da shahadar Muhammad Naim Nasser daya daga cikin manyan kwamandojinta.
Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar Laraba ne Isra’ila ta kai hari da jiragen sama na yaki a yankin Hosh da ke Taya a kudancin Lebanon.
A martanin da ta mayar kan wannan kisa, Hezbollah ta ce mayakanta sun harba makamin roka na Katyusha guda 100 a kan wasu wurare biyu na sojin Isra’ila a tuddan Golan da yahudawa suka mamaye,a matsayin wani bangare na martanin Hizbullah kan harin da kisan gilla da Isra’ila ta yi Muhammad Nasir Naim.
Wasu majiyoyin tsaro biyu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kwamandan da aka kashe shi ne ke da alhakin wani bangare na ayyukan Hizbullah a kan iyakar kasar Lebanon da Falastinu da yahudawa suka mamaye, inda kungiyar da sojojin Isra’ila ke fafatawa tun daga ranar 8 ga watan Oktoba.
Ana ci gaba da musayar wuta tun bayan da Isra’ila ta kashe babban kwamandan Hizbullah Sami Taleb Abdullah a watan Yuni. Wannan kisan gilla ne ya sa kungiyar Hizbullah ta harba jiragenta marasa matuka masu kunar bakin wake da kuma rokoki a kan sansanonmin sojin Isra’ila a matsayin ramuwar gayya.
Kungiyar Hizbullah ta bayyana karara cewa tsagaita bude wuta a zirin Gaza ita ce kadai hanyar da za ta kawo kwanciyar hankali a kan iyakar Lebanon da Falastinu da Isra’ila ta mamaye.