Ma’aikatar harkokin wajen kasar Labanon ta shigar da sabon korafi kan yahudawan sahyuniya gaban kwamitin sulhu na MDD, inda ta yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahyuniya suka kai kan kasar Labanon, da kuma keta hurimun ikon kasar, da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma yau fiye da watanni biyu.
Wannan korafin, wanda aka mika ta hannun wakilcin Dindindin na Labanon a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ya jibanci yadda Isra’ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar tun daga ranar 27 ga Nuwamba, 2024 ranar da tsagaita bude wuta ta fara aiki har zuwa yau Talata 4 ga Fabrairu.
Lebanon Ta yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama da yahudawan sahyoniya suka yi, da barnata gidaje da matsugunan jama’a, da yin garkuwa da ‘yan kasar Lebanon da sojoji, da kuma hare-haren da ake kai wa fararen hula da ke kokarin komawa kauyukansu da ke kan iyakar kasar ta Lebanon.
Kusan ‘yan kasar Lebanon 24 ne suka yi shahada sannan wasu fiye da 124 suka jikkata a cikin wannan lokaci.
Kan ne kasar Lebanon ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD musamman kasashen da suka dauki nauyi da shiga tsakani wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da su dauki kwararan matakai wajen tunkarar wadannan take-take, tare da yin matsin lamba kan Isra’ila ta mutunta dokokin kasa da kasa.