Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Hrin Wuce Gona Da Iri Na HKI

A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar

A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkata wasu da dama.

Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata.

Hare-haren sun shafi garin Kafar-Tabinet da kuma akan hanyar Kausariyyah al-siyadah.

Haka nan kuma jiragen na ‘yan sahayoniya sun kai wasu hare-haren a garin Ansariyyah, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane 6.

Hare-haren na HKI suna a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments