Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa, Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar.
Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya.
Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.
Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai.
A wani labarin daga Lebanon an bayyana cewa mutane 28 ne su ka yi shahada daga watan da ya gabata.
Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta, yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.”
A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne ƙasa ta tsaya musu.