Lebanon: Mutane 9 Sun Yi Shahada Wasu Kimanin 2,800 Sun Jikkata Bayan Wata Fashewa A Beirut

Rahotanni daga kasar Lebanon sun tabbatar da shahadar mutane akalla 9 tare da jikkatar wasu kimanin 2,800 bayan wata fashewa a birnin Beirut fadar mulkin

Rahotanni daga kasar Lebanon sun tabbatar da shahadar mutane akalla 9 tare da jikkatar wasu kimanin 2,800 bayan wata fashewa a birnin Beirut fadar mulkin kasar.

A cikin rahotonta, ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce akalla mutane tara ne suka mutu, yayin da wasu 2,800 suka samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa da aka fara bayar da rahoton a yankunan kudancin birnin Beirut.

Ma’aikatar ta ce “ana tura majinyata zuwa yankuna daban-daban a Lebanon saboda lamarin yafi karfin asibitocin yankin kudancin Beirut.

Daga cikin wadanda aka kashe har da wata yarinya ‘yar shekara 9 da kuma dan wani dan majalisa mai alaka da kungiyar Hizbullah, kamar yadda wakiliyar tashar talbijin ta Press TV a Beirut Mariam Saleh ta bayyana a wani rahoto daga babban birnin kasar Labanon.

An bayyana yarinyar mai suna Fatima Jafar Abdullah, shi kuma  saurayin shine Mahdi Ammar, dan wani dan majalisar wakilai Ali Ammar na kungiyar  Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon.

Jakadan Iran a Lebanon, Mojtaba Amani, shi ma yana cikin wadanda suka jikkata. Matarsa ​​ta yi amfani da shafin X, don tabbatar da rauninsa a lamarin, amma ta ce yanayin da yake ciki ba mai hadari ba ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments