Kungiyar Hizbollah ta sanar da kai hare-haren makaman roka da jirage marasa matuka kan sansanonin sojojin Isra’ila, da matsugunai da sojoji a arewacin Isra’ila.
Baya ga haka kuma kungiyar ta Lebanon ta ce ta kai hare-hare sau talatin da daya kan sojojin Isra’ila da sansanoninsu da kuma matsugunnensu da ke cikin falastinu da suka mamaye.
Kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa mayakanta sun kai hari kan sansanin sojojin Isra’ila na Tirat Carmel a kudancin Haifa, da sansanin Shraga kusa da Acre, inda suka yi amfani da makaman rokoki da aka bunkasa su.
Ta kuma ba da rahoton kai hari kan taron sojojin Isra’ila tara a kusa da Doviv da Sa’sa da Misgav da Yorn a arewacin Isra’ila.
Bugu da kari kan haka, ta ce ta kai hari kan wuraren sojojin Isra’ila 19 a kusa da garuruwan Maroun al-Ras da Markaba da Khiyam da Hanine da Talloussah a Lebanon.
Rahotannin kafofin yada labaran Haramtacciyar kasar Isra’ila sun ce an gano aƙalla makaman roka 40 da kuma jirage marasa matuka uku waɗanda aka harbo su daga Lebanon zuwa kudancin Isra’ila, abin da ya sa aka kunna jiniyar hare-haren sama a arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye.