Lebanon : Hare-haren Na’urorin Sadarwa Shelanta Yaki Ne, Zamu Mayar Da Martani   

Shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya ce fashe-fashen na’urorin sadarwa da Isra’ila ta kai a ranakun Talata da Laraba, wanda ya kashe mutane 37

Shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya ce fashe-fashen na’urorin sadarwa da Isra’ila ta kai a ranakun Talata da Laraba, wanda ya kashe mutane 37 tare da raunata kusan 3,000 a Lebanon, shelanta yaki ne.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya gabatar da yammacin Alhamis a jawabinsa na farko da aka watsa ta gidan talabijin tun bayan harin da ya ce makiya sun ketare duk wasu jajayen layukan da kuma dukkanin dokoki a wannan harin.

“Kisan gillar da aka yi a ranar Talata da Laraba laifi ne na yaki, shelanta yaki,” in ji shi, ya kara da cewa Isra’ila za ta fuskanci hukunci mai tsanani.

Wasu hare-haren, in ji shi, sun faru ne a asibitoci, kantin magani, kasuwanni, shagunan kasuwanci da ma gidajen zama, motoci jama’a da inda dubban fararen hula da suka hada da mata da kananan yara ke halarta.

Nasrallah ya ce, an kafa wani babban kwamitin bincike don yin nazari kan dukkan al’amuran.

A jawabin nasa, Hassan Nasrallah ya ce burin Isra’ila shi ne jefa tsoro a zukatan mutane, inda ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya.

“Idan dai har ba su daina hare-hare a kan Falasdinawa ba to ba za mu bar kudancin Isra’ila ba. 

Shugaban kungiyar ta Hezbollah, Hassan Nasrallah, ya ci alwashin hana Isra’ilawa komawa gidajensu a arewacin kasar.

Sojojin Isra’ilar dai sun ce suna shirin mayar da tsaro a arewacin kasar domin bai wa mutane damar komawa gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments