Sakatare-Janar na kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf Jassim Al-Badawi ya yi kakkausar suka kan amincewa da wasu kudirori guda biyu a majalisar Knesset ta Isra’ila da ke da nufin kakaba ikon Isra’ila kan yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye.
A rahoton talabijin ta Aljazeera, Jassim Al-Badawi a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis ya jaddada cewa, matakin da majalisar Knesset ta Isra’ila ta dauka, wani mataki ne da ya saba wa kudurorin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samun zaman lafiya mai dorewa.
Haka nan kuma ya jaddada cewa ayyukan gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan suke yi a fili take ga hakkokin tarihi na al’ummar Palastinu da dokokin kasa da kasa ne.
Sakatare-janar na kwamitin hadin gwiwar kasashen yankin Gulf ya yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin da suka rataya a wuyansu tare da matsa lamba a kan mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da wadannan ayyuka masu hadari da kuma kara gurgunta harkokin tsaro da zaman lafiyar yankin.
Al-Badawi ya nanata matsayar kwamitin hadin gwiwa na yankin tekun Fasha na goyon bayan al’ummar Palasdinu da halalcin ‘yancinsu na kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
A ranar Laraba, Majalisar Knesset ta Isra’ila ta amince da wasu kudirori biyu: daya na mayar da yankin yammacin kogin Jordan kaco kaf a karkashin ikon Isra’ila, daya kudirin kuma za a hade matsugunan yahudawa na Ma’aleh Adumim da yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Kudus.