Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar

A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan

A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.

Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Khartum da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.

Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments