Kwamnadan Dakarun IRGC Yace Sojojinsa A Shiye Suke Su Kare Kasar Daga Makiya

Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin

Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare.

Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake wani Jawabi a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran.

Janar Salami yana wannan maganane bayan da shugaban kasar Amurka Dunal Trump wanda yake ziyarar wasu kasashen larabawa a yankin yammacin Asiya, na cewa idan an kasa cimma dai-daito tsakanin Iran da Amurka a tattaunawa kan shirinta na makashin nukliya to Iran ta shiryawa yaki.

Salami ya kara da cewa sun san makiyan JMI a wannan yankin, a duk lokacinda hanyoyin tattaunawa da Diblomasiyya sun kasa kaiwa ga fahintar juna to kuwa sojojin kasar Iran musamman dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar a shirye suke su kare kasar da kuma mutuncinta.

Manjo Janar Salami ya bayyana cewa: Karfin sojoji da kuma dakarun kare juyin juya halin musulunci karuwa yake a ko wace shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments