Kwamitin Tsaro Na AU Yai Yi Zaman Gaggawa Kan Halin Da Ake Ciki A Gabashin DRC

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC).

Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC.

Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan tawayen M23 sun kwace iko da birnin na Goma mai muhimmanci a Kongo.

 ‘Yan tawayen na M23, waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun zafafa hare-hare a gabashin Kongo a makon jiya, inda suka kwace muhimman birane, Sai dai Shugaban Rwanda Paul Kagame ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ‘yan tawayen.

Shugaban Kenya William Ruto, wanda yake shugabancin kasashen Gabashin Afirka ya sanar a ranar Lahadi cewa, kungiyar za ta gudanar da wani taro na musamman a cikin sa’o’i 48 don tunkarar rikicin da yake yaduwa a Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo.

Ruto ya tabbatar da cewa tun da farko ya tattauna da Shugaban DRC Kongo Felix Tshisekedi da Shugaban Rwanda Paul Kagame, wadanda dukkansu suka amince za su halarci taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments