Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da jibge sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya ta Afirka a kasar Somaliya
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma’a ya amince da matakin tura sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka zuwa Somaliya, wanda zata maye gurbin rundunar da ke da alaka da kungiyar a kasar, wanda sabuwar rundunar zata fara aiki a farkon shekara mai zuwa ta 2025, da nufin yakar mayaka masu da’awar jihadi a kasar na Al-Shabab.
Wannan sabuwar rundunar dai ana kiranta da kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AUSOM, kuma za ta gudanar da aiki ne na tsawon shekara daya, sannan za ta maye gurbin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka ta (ATMIS) wadda ta samu amincewar jami’an kwamitin sulhun Majalisar ta Dinkin Duniya a shekara ta 2022 don yakar abin da ta kira masu jihadi har zuwa karshen 2024.
Kwamitin Sulhu ya amince da matakin kafa sabuwar rundunar ce da akasarin kasashe 14 daga cikin kasashe 15 suka kafa, inda wata kasa ta kaurace wa kada kuri’a, wato Amurka, wacce ta danganta matsayinta game da tsantsenin gabatar da tallafin kudi ga wannan runduna.