Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana goyon bayan kungiyoyin da suke zagon kasa a kan iyakar Iran
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Bisa binciken da aka gudanar, an samu tabbacin cewa; Yahudawan sahayoniyya suna goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke kan iyakar Iran da kuma gudanar da ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kan iyakokin kasar.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: A yakin da ake yi a yau a bangarori daban-daban da gungun ‘yan ta’adda da masu adawa da juyin juya halin Musulunci da al’ummar kasa, ya sha bamban idan aka kwatanta da baya. Ya kara da cewa: A ‘yan watannin da suka gabata, sun ga irin hare-haren ta’addancin da aka kai kan ofisoshin ‘yan sanda da kuma kan iyakokin kasar, inda aka tabbatar da cewa ba wata kungiya ce kawai take kai wadannan hare-hare ita kadai ba, lallai akwai hannun jami’an leken asiri masu karfi a bayansu, inda suke aiki da su kafada da kafada don cimma burinsu.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Yunkurin da ake yi a kan iyakokin kasar Iran yana nuni da shirin makiya da kuma karfafa kungiyoyin makiya a kan iyakokin kasar, kuma bisa binciken da aka gudanar, yahudawan sahayoniyya suna goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda a kan iyaka da kuma ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kan iyakokin.