Kwamandan Sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Ce Rusa Kungiyar Hamas Zai Dauki Shekaru

Wani kwamandan sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Rusa kungiyar Hamas yana bukatar shafe tsawon akalla shekaru biyu Ma’aikatar lafiya a Zirin Gaza ta

Wani kwamandan sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Rusa kungiyar Hamas yana bukatar shafe tsawon akalla shekaru biyu

Ma’aikatar lafiya a Zirin Gaza ta sanar da shahadar Falasdinawa akalla 69 sakamakon luguden bama-bamai da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a Zirin Gaza a cikin sa’o’i da suka gabata. Ma’aikatar ta ce adadin wadanda suka yi shahada ya kai sama da mutane 37,800 sannan wadanda suka jikkata sun haura zuwa 86,800.

A rana ta 267 da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka shafe suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza, inda ya janyo shahadan Falasdinawa kimanin 40,000 tare da jikkatan wasu kimanin 90,000, sannan kuma yankin ya koma baraguzai, wani kwamandan sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya fito yayi furuci da rashin yiwuwar kawar da kungiyar Hamas, inda ya kasance daga cikin jerin kwamandojin sojin haramtaciyyar kasar Isra’ila da suka amince da rashin yiwuwar shafe kungiyar Hamas, kuma shi ne kwamandan runduna ta 12 a rundunonin sojojin mamaya, wanda ya yarda da cewa manufar kawo karshen kungiyar Hamas, ba abu ne mai sauki ba, kuma rusa kungiyar yana bukatar tsawon akalla shekaru biyu.

Wannan ikirari ba kawai ya gurgunta kwarin gwaiwar gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ba ne kadai, har ma ya rusa fatan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke kewayen Zirin Gaza, kuma furucinsa ya zo ne a daidai lokacin da yake magana kan karfin da ‘yan gwagwarmaya suke da shi ne wajen ci gaba da harba makaman masu linzami kan haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments