Kwamandan Rundunar Sojin Saman Iran Ya Ce: Iran Ta Kai Matsayin Dogaro Da Kanta A Fagen Kere-Kere

Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja Kwamandan rundunar sojin

Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja

Kwamandan rundunar sojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa: Sojojin saman Iran na ma’aikatar tsaro da taimakon sojojin kasar sun cimma mataki dari bisa dari a fagen gudanar da kere-keren kayayyakin da suke bukata a harkar tsaron kasa, kuma dukkanin kayan aikin wannan runduna an inganta su tare da mayar da su saffarin cikin gida.

A ranar Juma’a 7 ga watan Fabrairu, Birgediya Janar Wahidi ya sanar a gaban taron kwamandojin sojojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jagoran juyin juya halin Musulunci a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin cewa: Sojojin sama da na tsaron sararin samaniya su ne manyan makamai biyu na sojojin kasar Iran, kuma duk da takunkumin da aka kakaba musu, sun samu nasarar kare kasar tsawon shekaru takwas a tsawon kare kai daga yakin wuce gona da iri da aka kaddamar kanta a farkon samun nasarar juyin juya halin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments