Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Jinjinawa Dakarun Yemen Kan Yadda Suke Kare Falasdinawa

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun bayyana cewa: Hare-haren makamai masu linzami da Yemen yake kai wa kan Isra’ila sun shige tunanin masana yahudawan sahayoniyya da na’urorinsu

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun bayyana cewa: Hare-haren makamai masu linzami da Yemen yake kai wa kan Isra’ila sun shige tunanin masana yahudawan sahayoniyya da na’urorinsu na zamani

Kwamitin kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ya bayyana cewa: Hare-haren makamai masu linzami da jaruman sojojin Yemen da Dakarun gwagwarmayar kasar suke kai wa cikin tsakiyar yankunan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya wadanda suke yin sanadin halaka da jikkatar ‘yan sahayoniyya masu yawa baya ga barnata dukiyoyi, lamari ne da yake ci gaba da rikita lissafin yahudawan sahayoniyya tare da rikita tunaninsu gami da karyata da’awar jagororin ‘yan mamaya na ikirarin cewa sun gano sirrin lamarin.

Kwamitin ya kara da cewa: Hare-haren makamai masu linzami na Yemen masu albarka suna nuni da irin azamar da al’ummar Yemen suka yi da jajircewar shugabanninsu wajen kara ba da goyon baya ga Gaza bisa wajibin addini da na jin kai, kamar yadda jagoran juyin juya halin Yemen Sayyid Abdul-Malik Badruddeen Al-Houthi ya tabbatar.

‘Yan gwagwarmayar Falastinawa sun jaddada cewa: Ci gaba da goyon bayan kasar Yemen da dogewarsu kan gudanar hare-haren daukan fansa suna ruda lissafin ‘yan sahayoniyya, tare da kawar da has ashen nasarorin da jagororin ‘yan mamaya suke ikirarin cimmawa, da kuma tabbatar da babbar gazawar ‘yan sahayoniyya wajen cimma munanan manufofinsu. Musamman yadda su da kansu suke bayyana rashin iya fuskantar makamai masu linzami na Yemen da haka ke tabbatar da raunin tsarin tsaronsu na soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments