A wani bayani da kungiyar Hizbullah ta fitar a jiya Alhamis ta yi Allawadai da hare-haren da sojojin HKI su ka kai wa kasar Yemen, tare da cewa, babu wani zabi da ya rage idan ba turjiya,tsayin daka da gwgawarmaya ba.
Bayanin na Hizbullah ya cigaba da cewa, wuraren da aka kai wa hare-haren na fararen hula ne da cibiyoyin tattalin arziki da hakan karya dokokin kasa da kasa ne.
Har ila yau bayanin na kungiyar Hizbullah ya ce, sojojin na HKI sun kai wadannan hare-haren ne dai bayan da su ka ci kasa a gaban harin da Yemen take kai musu domin taimakawa al’ummar Falasdinu da kare ‘yancinsu.
Ita ma kungiyar Hamas ta yi tir da harin na abokan gaba akan Yemen wanda su ka kai wa filin saukar jiragen sama na Sanaa da kuma tashar jiragen ruwa ta Hudaidah.
Kungiyar ta Hamas ta kuma ce abinda ‘yan sahayoniyar su ka yi, cigaba ne da siyasar nuna karfi da ta’addanci akan al’ummomin Falasdinu da kuma na wannan yankin a karkashin kariyar Washington da wasu kasashen turai.
Haka nan kuma Hamas ta jinjinawa Yemen, akan matakin da take dauka na nuna goyon bayan Falasdinawa, suna masu jaddada cewa, hare-haren na Isra’ila da kasashen turai ba za su hana su cigaba da nuna goyon bayan Falasdinawa ba.
Ita ma kungiyar “ Popula Front” ta fitar da bayani na yin Allawadai da harin na HKI akan kasar Yemen, tare da bayyana shi a matsayin aikin ‘yan ta’adda,’yan mulkin mallaka.
Ita kuwa kungiyar “Ftaha-Intifadha” ta ce;harin halayya ce ta ‘yan dabar sahayoniya.