Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare.
Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin.
Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan mutanen Gaza da al’ummar Falasdinu.
Kwamitin al’umma na goyon bayan gwgawarmayar al’ummar Falasdinu ya bayyana harin na Amurka da Birtaniya akan Yemen da cewa, nuna goyon bayan ne karara ga HKI.
Bayanin ya kuma ce; Maharan ba za su karya kashin bayan al’ummar Yemen ba da suke tsayin daka wajen taya Falasdinawa fada da kalubalantar killace mutanen Gaza da HKI ta yi, bisa goyon bayan Amurka.
Ita kuma kungiyar “Harkatul-Mujahidin” ta yi kira ne ga rayayyun al’ummu da ‘yan gwgawarmaya da su hada karfi da karfe domin fuskantar wuce gona da irin ‘yan sahayoniya da Amurka, tare da kara da cewa; Babu abinda zai takawa masu daga hancin da girman kai, birki,sai karfi.