Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai

Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza

Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai fafatukar ‘yantar da Falasdinu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, inda suka bayyana matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda suka yi maraba da gwagwarmayar al’ummar Falastinu, musamman a Gaza wajen fuskantar laifukan yahudawan sahayoniyya.

Kungiyoyin Hamas da na sauran kungiyoyin Falasdinu sun yaba da jarumtar gwagwarmayar da ta janyo hasara ga makiya, suna masu jaddada cewa: “Muradin jama’a da ‘yan gwagwarmaya ya fi duk wani yunkuri na murkushe su.” Har ila yau, sun jinjinawa “bangarori masu goyon bayansu a Yemen, Lebanon, Iran, da Iraki saboda goyon bayan da suke ba wa Falasdinawa.”

Sun gode wa masu shiga tsakani na Masar, Qatar, da Turkiyya, da kuma duk wadanda suka ba da gudummawar goyon bayan shawarwarin, suna mai kira ga Amurka da masu shiga tsakani da su ci gaba da bin sharuddan yarjejeniyar da kuma hana kaucewa daga kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments