Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira

Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa

Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira.

Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu.

Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan  fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka nan ita kanta wannan maganar tana nufin shelanta wani sabon yakin akan al’ummar Falasdinu da hakan yake da bukatar fitar da wani matsayin na kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa.

A karshe sun bukaci ganin cewa taron kasashen larabawa da za a yi nan gaba kadan, ya fito da wani tsari na ci gaban al’umma, saboda kawo karshe duk wani batu na yin hijira. Haka nan kuma sun bukaci ganin masu alaka da ‘yan mamaya daga cikin larabawa sun yanke ta.

Jami’in da yake kula da tuntubar juna a tsakanin kungiyoyi mabanbanta Khalid al-Badhash ya bayyana cewa; Duk da baranazar da hakkokin falasdinawa suke fuskanta, da kuma makirece-makircen Amurka, sai dai kuma batun kare hakkokin Falasdinawa ya sake dawowa da karfi a duniya, kuma duniyar ta gane hakikanin ‘yan mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments