Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai A Arewacin Afganistan

Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla

Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 5 da kuma raunata wasu da dama.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Daesh Khorasan” tana fadar haka a shafinta na sadarwa, bayanda wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da wani banki a garin Kunduz, wanda ya halaka shi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar.

Labarin ya kara da cewa an kai harin kunan bakin wakenne da misalign karfi 8:35 na safe a yau Laraba, wato 4:05 na safe agogin GMT.

Mai gidan bankin da kuma wasu mutane 4 daga cikin akwai fararen hula da kuma wani mamba a jam’iyya mai mulkin kasar, ta kungiyar Taliban.

Kakakin yansandan lardin Kunduz Jumma Uddin Khakasr ya ce: Banda wadanda suka rasa rayukansu, akwai mutane 7 da suka ji rauni. Amaq ya ce, sun tada bom din ne kusa da jami’an yansanda na lardin wadanda suke jiran karban albashinsu.

Kungiyar ta ce, daruruwan mutane ne suka kashe a harin. Kungiyar Daesh Khurasan dai ta sha daukar alhakin kai hare-hare iri wannan a kasar ta Afganistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments